Nothing Special   »   [go: up one dir, main page]

Jump to content

Nasarawa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Nasarawa


Wuri
Map
 8°32′N 8°18′E / 8.53°N 8.3°E / 8.53; 8.3
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birni Lafia
Yawan mutane
Faɗi 2,523,395 (2016)
• Yawan mutane 93.06 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Yawan fili 27,117 km²
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Jahar pilato
Ƙirƙira 1 Oktoba 1996
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa Majalisar Zartarwa ta Jihar Nasarawa
Gangar majalisa Majalisar Jihar Nasarawa
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2 NG-NA
Wasu abun

Yanar gizo nasarawastate.gov.ng
Lambar motar Nasarawa
logon hoton jihar Nasarawa
Fayil:Engineer AA Sule.jpg
A Sule Gwamnan jihar nasarawa
babban gate na jami'ar jaha
Lighthouse and mascot nasarawa 2017
tree of thorns nasarawa state Nigeria
nasarawa lafiya

Jihar Nasarawa: jiha ce dake, a Arewa ta tsakiyar ƙasar Najeriya. Tana da yawan filaye kimanin kilomita murabba’in 27,117 da yawan jama’a miliyan ɗaya da dubu ɗari takwas da sittin da tara da ɗari uku da saba'in da bakwai (ƙidayar shekara ta 2006). Babban birnin tarayyar jihar shi ne Lafia. Abdullahi Sule, shi ne gwamnan jihar tun zaɓen shekara ta 2011, har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shine Emmanuel Akabe. Dattijai a jihar sun haɗa: Philip Aruwa Gyunka, Abdullahi Adamu da Suleman Asonya Adokwe.

Hanyar iyakar abuja da kuma keffi nasarawa state

Jihar Nasarawa tana da iyaka da jihohi huɗu: Plateau, Kogi, Taraba, Benue da Abuja.

Karachi waterfall Nasarawa state

Ƙananan hukumomi

[gyara sashe | gyara masomin]

Jihar Nasarawa nada adadin ƙananan hukumomi guda goma sha uku (13),ga kowanensu tare da kuma adadin yawan Mutanen dake a Ƙaramar hukumar. (Ƙidayar ahekara ta 2006)[1]:

[gyara sashe | gyara masomin]
Shiyar Sanata ta Yamma a Nasarawa 716,802 Shiyar Sanata ta Arewa a Nasarawa 335,453 Shiyar Sanata ta Kudu a Nasarawa 811,020
Karu 205,477 Akwanga 113,430 Awe 112,574
Keffi 92,664 Nasarawa Egon 149,129 Doma 139,607
Kokona 109,749 Wamba 72,894 Keana 79,253
Nasarawa 189,835 Lafia 330,712
Toto 119,077 Obi 148,874

Labarin Yanayi

[gyara sashe | gyara masomin]

Nasarawa tana da yanayi mai zafi mai zafi da savanna. Yanayin zafin birnin na shekara shine 29.39°C (84.9°F) kuma ya kan yi ƙasa da -0.07% idan aka kwatanta da na Najeriya. Nassarawa na samun hazo kusan milimita 136.71 (inci 5.38) kuma tana da kwanaki 155.37 na ruwan sama (42.57% na lokacin) kowace shekara.

A jihar Nasarawa, lokacin rani yana da danshi kuma wani bangare na gajimare, kuma ana yin zafi duk shekara. Lokacin damina yana da tsauri da yawa. Matsakaicin zafin jiki na shekara-shekara yana daga 63 zuwa 95 digiri Fahrenheit, da wuya yana faɗuwa ƙasa da 57 ko sama da 101.

Daga ranar 29 ga Janairu zuwa 14 ga Afrilu, lokacin zafi, tare dkuma a matsakaita yawan zafin rana da ya wuce 93°F, yana ɗaukar watanni 2.5. Watan da ya fi zafi a jihar Nasarawa a duk shekara shi ne Maris, inda matsakaicin zafin jiki ya kai 95°F, kuma mafi karancin zafin jiki ya kai 74°F.

Lokacin sanyi na watanni 3.7, wanda ke gudana daga Yunin shekarar 22 zuwa 13 ga Oktoba, yana da matsakaicin zafin rana na ƙasa da 85°F. Nasarawa ta fuskanci wata mafi sanyi a cikin shekara a cikin Disamba, tare da matsakaicin yanayin ƙasa na 64 ° F da mafi girma 89 ° F.

Ma'adanai a jihar basarawa sun haɗa da;[2]

  • Ma'adanin Baryte
  • Ma'adanin Bauxite
  • Ma'adanin Coal
  • Ma'adanin Dolomite
  • Ma'adanin Sapphire
  • Ma'adanin Talc
  • Ma'adanin Quartz
  • Ma'adanin Tantalite
  • Ma'adanin Tourmaline
  • Ma'adanin Mica
  • Ma'adanin Iron
welcome to nasarawa

Jihar Nasarawa naɗa makartun masu yawa , waɗanda suka hada da kamarantun primare, sakandare dakuma makarantun gaba da sakandare:

Makaratn gaba da Sakandare

[gyara sashe | gyara masomin]

Mafiya yawan al'umar dake zaune a jihar Nasarawa Musulmai ne[6] ko Kuma kiristoci[7], amma akwai kaɗan da suke addinin Mazuganci

Adadin Al'umma

[gyara sashe | gyara masomin]

Jihar Nasarawa naɗa adadin mutane 1,869,377 a kididdigar shekara ta 2006, wanda hakan ya bawa jihar zama ta biyu a yawan al'umma bayan jihal Bayelsa[8]

Jihar Nasarawa tana gudana a ƙarƙashin gunadar wa ta gwamnan jihar Abdullahi Sule[9], wanda shike jagoran sauran ayyuka na jihar. Garin na dauke da yan-majalisu, da wasu mukarraban gwamnati

Wuraren Bude Ido

[gyara sashe | gyara masomin]

Jihar Nasarawa nada wurareb shakatawa da kuma bude ido masu yawa , wasu daga ciki sunhaɗa da

Sanannun Mutane

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Imam Sulaiman-Ibrahim Former Director General of NAPTIP[12]
  • HRH Alhaji Abdullahi Amegwa Agbo Osana of Keana[13]
  • HRH Alhaji Ahmadu Aliyu Ogah Andoma of Doma[14]
  • Sen. Abdullahi Adamu Natinal Chairman APC[15]
  • Suleman Odapu Public Relation Practitioner

Yare/Kabilu

[gyara sashe | gyara masomin]

Jihar Nasarawa bada kabilu ma bam-banta guda 25 , sanannu daga cikinsu sun hada da

  1. 2006 Population Census, Federal Republic of Nigeria, National Bureau of Statistics. Archived from the original Archived 2007-07-04 at the Wayback Machine on 2009-03-25.
  2. https://nigerianembassythehague.nl/about-nigeria/natural-resources/
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-10-27. Retrieved 2023-01-06.
  4. https://myschool.ng/classroom/institution-courses/federal-polytechnic-nasarawa
  5. https://www.myschoolgist.com/ng/fulafia-courses/
  6. https://tribuneonlineng.com/nasarawa-school-graduates-7-honours-4-muslims-for-contributions-to-islam/
  7. https://duniyarmuayau.com.ng/2020/12/25/me-ya-faru-da-mabiya-addinin-kirista-a-jihar-nasarawa-shugaban-ƙaramar-hukumar-lafia/[permanent dead link]
  8. https://web.archive.org/web/20110519235026/http://www.population.gov.ng/files/nationafinal.pdf
  9. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-01-06. Retrieved 2023-01-06.
  10. http://www.globalpost.com/webblog/nigeria/dreaming-farin-ruwa
  11. https://thenationonlineng.net/mission-to-maloney-hill/
  12. https://newsdiaryonline.com/sulaiman-ibrahim-assumes-office-as-head-refugees-commission/
  13. https://www.blueprint.ng/osana-of-keana-five-years-of-impactful-royalty/
  14. https://emporiumreporters.com.ng/tag/hrh-alhaji-ahmadu-aliyu-ogah-onawo/
  15. https://www.premiumtimesng.com/news/headlines/519885-profile-of-new-apc-national-chairman-abdullahi-adamu.html
  16. https://www.premiumtimesng.com/opinion/135496-nasarawa-massacre-barbarians-on-rampage-by-dele-agekameh.html


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara