Wikipedia:Tutorial
Gabatarwa | Rajistar account | Yadda ake gyaran Wikipedia | Yadda ake mahadar shafi | Bada madogarar bincike | Shafukan tattaunawa | Manufofin Wikipedia | Karin bayani |
Wannan shafukan dake tafe suna dauke da muhimman bayanai akan yadda ake gyaran Wikipedia.
Manufar Wikipedia shine ta tattaro ilimin ɓangarori da dama wanda ya shafi dukkan ilimin ɗan adam domin amfanar da al'umma. Dukkan bayanan dake akan Wikipedia dole ne ya zama gaskiya ne, sannan kuma an bada madogarar inda aka samo.
Wikipedia tana maraba da kowa, kuma tana ba kowa damar bada gudummuwar sa wajen wannan aiki.
Wikipedia tana da wasu manufofi sannan ita ba wuri bane na talla ba, kowace iri. Wikipedia tana bada bayani akan mutane sanannu a tarihi amma ba ta tallata su ba, hakazalika, kamfanoni, masa'na'antu, da duk wani abu da ɗan adam ya kintace a kundayen ilimi da aka riga aka rubuta.
Waɗannan bidiyoyin guda biyu, bidiyoyine da suke bayani akan Hausa Wikipedia da kuma Wikipedia a jimlatance, bidiyan farko bidiyo ne da wasu daga cikin ƙwararrun editocin Hausa Wikipedia suke bayani cikin hikima ta hanyar tambaya da kuma amsa akan Wikipedia da kuma Hausa Wikipedia, kuma suna bayanin ne a sauƙaƙe a cikin harshen Hausa. Bidiyo na biyu kuma yana bayani ne akan ta hanyan da edita zai bi wajen yin editin a Wikipedia, wasu ƙwararrun editoci ne suke bayanin a cikin harshen Hausa.
-
Amsoshi da kuma tambaya akan Wikipedia a cikin Harshen Hausa.
-
Gajeran bidiyo na turanci dangane da gyara a Wikipedia
Wadannan bidiyoyi ne da zasu taimaka ma Hausawa sanin hanyoyin da zasu bi wajen gudanar da sauye-sauye da kuma gyara a Hausa Wikipedia, Bidiyoyin zasu taimaka ma sababbin editoci sanin hanyar da zasu bi wajen koyan editin cikin sauki a Wikipedia. Kowanne bidiyo a cikin nan yana da darasin da yake koyarwa, idan kana da buƙatan ƙarin bayani ko kuma neman wasu bidiyoyi, zaka iya ma wannan magana a shafin shi na tattaunawa Anasskoko. Waɗannan bidiyoyin dake ƙasa bidiyoyi ne da zaka koya yanda ake ƙirƙiran shafi/muƙala wato (article) a Wikipedia.
-
Yanda ake ƙirƙiran muƙala wato (article) 01
-
Yanda ake ƙirƙiran muƙala wato (article) 02
-
Yanda ake ƙirkiran mukala wato (article) 03
-
Yanda akeƙirƙiran muƙala wato (article) 04
Idan kai mutun ne ma'abocin karance-karance zaka iya duba PDF na koyan yanda zaka ƙirƙira mukƙala a Hausa Wikipedia, ka sauke manhajar PDF din a cikin wayarka.
-
PDF akan yanda ake rubuta muƙala (article)
-
PDF dake ɗauke da (Bayani akan cikin Hausa Wikipedia)
Waɗannan wasu daga cikin bidiyoyi ne da su taimaka ma edita wajen sanin hanyar da zai bi wajen saka hoto a WP:Wikimedia Commons da kuma yanda saka hoto a muƙala wato (article), da wasu bidiyoyi ma da zasu taimaka wajen koyama edita abubuwa da yawa.
-
Yanda zaka saka hoto a Wikimedia Commons
-
Yanda zaka saka hoto a muƙala
-
Bayani akan Hausa Wikipedia
-
Bayani na biyu mai muhimmanci akan WP:Hausa Wikipedia
Idan kuna bukatan wasu muhimman bayanai ku duba a waɗannan shafukan Manufofi Biyar | Visual editor | Yadda ake rubuta muƙala | Rubutu a mahangar da ba son rai | Ingancin tushen bayanai