Kamala Harris
Kamala Devi Harris (an haife ta a ranar 20 ga watan Oktoba, a shekara ta alif dari tara da sittin da hudu miladiyya 1964), 'yar siyasar Amurka ce kuma lauya. Ita ce mataimakiyar shugaban kasar Amurka ta 49. Ta yi aiki a matsayin Sanatan Amurka daga Kalifoniya daga shekarar (2017) har zuwa (2021) Kafin ta hau kujerar Sanata, Harris ta kasance Babbar Mai Shari’a ta Jiha daga shekara ta (2011 ) zuwa shekara ta (2017)
A ranar 21 ga watan Janairu, shekara ta (2019) Harris ta sanar da takararta ga Shugaban Amurka a zaben shekarar (2020) Ta gama kamfen dinta a ranar 3 ga watan Disamba, shekara ta (2019) Bayan Joe Biden ya lashe zaben, sai ya zaɓi Harris a matsayin abokiyar takara a matsayin Mataimakiyar Shugaban kasa. Sun kuma lashe zaben ne a ranar 7 ga watan Nuwamba.
Rayuwar farko
[gyara sashe | gyara masomin]An kuma haifi Harris a Kaiser Permanente Oakland Medical Center a Oakland, California. Ta tashi ne a Tamil Indian American kuma Jamaican American. Iyaa yenta su ne Shyamala Gopalan Harris (haifaffiyar Tamilil na Chennai da Donald Harris. Dukansu Shyamala da Donald Harris sun yi karatu a Jami'ar California, Berkeley. Iyayen Harris sun sake aure a shekarar alif ta (1971) kuma a shekarar alif ta (1976) Harris ya koma Kanada tare da mahaifiyarsa da 'yar'uwarta. Harris ya tafi kwaleji a Jami'ar Howard a shekarar alif ta (1986) kuma ya sami digiri a kimiyyar siyasa.
Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin shekarar alif ta (1989) Harris ta zama lauya bayan karatu a Hastings College of Law a Jami'ar California. Ta yi aiki a ofishin Babban Lauyan Gundumar Alameda a shekarar alif ta (1990) A shekarar (1998) Harris ta bar aiki don ofishin Babban Lauyan Gundumar a San Francisco. A cikin shekara ta (2003) Harris ta zama Babban Lauyan San Francisco.
Ta yi aiki a matsayin Babbar Lauyan California har zuwa shekara ta (2017) lokacin da ta zama Sanata a California.
Takarar Sanatan 2016
[gyara sashe | gyara masomin]A farkon shekara ta (2016) Harris ta ce za ta yi yunkurin zama sanata bayan Barbara Boxer ta ce ba za ta yi aiki a matsayin sanata ba a zango na gaba. Harris ta ci matsayin a shekara ta (2016) kuma ta zama sanata a ranar 3 ga watan Janairun shekara ta (2017).
2020 yakin neman zaben shugaban kasa
[gyara sashe | gyara masomin]Har ranar 21 ga watan Janairu, a shekara ta (2019) a hukumance ta sanar da kamfen dinta na Shugaban Amurka a zaben shugaban kasar Amurka na shekara ta (2020) Bayan watanni na faduwar lambobin zabe da karancin kudin yakin neman zabe, ta kuma kawo ƙarshen yakin neman zaben nata a ranar 3 ga watan Disamba, shekarar ta (2019).
A watan Agusta 11, shekara ta (2020) Biden ya zabi Harris a matsayin abokin takararsa. A ranar 7 ga watan Nuwamba, tikitin Biden-Harris ya doke tikitin Trump - Pence wanda ya sanya ta zama zababben Mataimakin Shugaban kasa.
Kyauta da girmamawa
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin shekara ta (2020) Harris da Biden an ba su suna Mutanen lokaci na Shekara.