Abdul Bashiru
Abdul Bashiru | |||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||
|
Abdul Bashiru (an haife shi a ranar 17 ga watan Afrilun shekara ta 1992), ƙwararren ɗanɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Ghana wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan baya na hagu a ƙungiyar Premier ta Ghana Ashanti Gold.[1]
Aikin kulob
[gyara sashe | gyara masomin]A baya Bashiru ya yi cinikinsa da kulob ɗin Dreams FC da ke Accra kafin ya koma Ashanti Gold. Ya taɓa yin wasa a ƙungiyoyin Ghana; Hearts of Oak, King Faisal, Bechem United, Sekondi Eleven Wise, Inter Allies da kuma Masari kulob Ismaily SC .[2]
Dreams FC
[gyara sashe | gyara masomin]Ya taimaka wa kulob ɗin samun ci gaba a gasar Premier ta Ghana a kakar shekara ta 2014-2015. Ya buga wasa a Dreams na tsawon shekaru 6 kuma ya zama kyaftin a ƙungiyar a gasar firimiya ta Ghana ta shekara ta 2016 wanda shi ne karon farko da suka fara buga gasar ta Ghana. [3][4] Ya buga wasanni 25 kuma an zaɓe shi a matsayin gwarzon ɗan wasan Premier na Ghana wanda ya fafata da Latif Blessing da Kwesi Donsu .[5] Daga baya Liberty Professionals 'Laif Blessing ne ya lashe kyautar. An kuma zaɓen shi a matsayin wanda ya fi kowanne dan wasan baya na bana kyautar.[6][7][5] An kuma ba shi kyautar gwarzon ɗan wasan ƙungiyar a kakar wasa ta bana. [4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "The ultimate 18-team Ghana Premier League season guide 2020/21 - MyJoyOnline.com". www.myjoyonline.com (in Turanci). Retrieved 2021-02-17.
- ↑ "OFFICIAL: Dreams FC farm out skipper Abdul Bashiru to Bechem United on a season loan". Modern Ghana (in Turanci). Retrieved 2021-03-19.
- ↑ "Bechem United defender Abdul Bashiru moves to Kosovo to join FK Prishtina". GhanaSoccernet (in Turanci). 2017-07-21. Retrieved 2021-03-20.
- ↑ 4.0 4.1 "Dreams FC vote captain Abdul Bashiru as club's player of the season". Modern Ghana (in Turanci). Retrieved 2021-03-19.
- ↑ 5.0 5.1 "Latif Blessing, Kwesi Donau and Abdul Bashiru battle it out for 2015/16 GPL player of the season". Modern Ghana (in Turanci). Retrieved 2021-03-19.
- ↑ "Dreams FC captain Abdul Bashiru joins Bechem United on loan". www.ghanaweb.com (in Turanci). 2017-01-14. Retrieved 2021-03-19.
- ↑ "OFFICIAL: Dreams FC captain Abdul Bashiru joins Bechem United on loan - Kickgh.com". www.kickgh.com (in Turanci). Archived from the original on 2023-03-21. Retrieved 2021-03-19.
Hanyoyin haɗi na waje
[gyara sashe | gyara masomin]- Abdul Bashiru at Global Sports Archive
- Abdul Bashiru at Soccerway