Nothing Special   »   [go: up one dir, main page]

Jump to content

Barack Obama

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sake dubawa tun a 15:35, 2 Nuwamba, 2011 daga FoxBot (hira | gudummuwa) (r2.7.2) (Robot: Adding nso:Barack Obama)
Barack Obama
Barack Obama
shugaban Amurika na 44
Lokacin da yazama shugaba 20 Jauwari 2009
ya karbi ragamar mulki daga George W. Bush
mataimake Joe Biden
Byrdstede: Honolulu, Hawaii
matarsa Michelle Obama
Þingliċ Ȝefere: Democratic
Underforesittend: Joe Biden

An aifi Barack Hussain Obama ranar 4 ga watan Oguster na shekara ta 1961 a birnin n Honolulu dake yankin Hawai a ƙasar Amurika. Tun yana ɗan shekaru biyu da aihuwa iyayensa suka rabu, ya cigaba da zama tare da ma´aifiyarsa. Ubansa musulmi ƙan kasar Kenya a nahiyar Afirka, ya bar Amurika bayan ya rabu da matarsa ba´amurka inda ya koma gida Kenya, ya kuma zama minister a cikin gwamnatin shugaban ƙasa na farko, wato Jomo Keniyatta, kamin Allah ya amshi ransa, a shekara ta 1982 a cikin haɗarin mota.

A lokacin da ya samu shekaru shida, har zuwa shekaru 10, Barack Obama ya bi ma´aifiyarsa a ƙasar Indonesia inda suka yi zama na shekaru huɗu. Sai a shekara ta 1971 ya komo Honolulu, inda ya ci gaba da karatu. Yayi karatu a jami´ar Kaliforniya da kuma ta Kolumbiya a birnin New York. Bayan ya kamalla karatu, a jami´a, Obama ya fara aiki a matsayin jami´i, ta fannin lissafin kudi. To saidai ba jima ba yana wannan aiki ya kuma koma ƙarin ilimi, inda a shekara ta 1991 ya fito da digrin digirgir ta fannin sharia´a. Barack ya jima ya na kwaɗayin shida siyasa, amma sai a shekara ta 1996 haƙƙarsa ta cimma ruwa, inda karon farko a ka zaɓe shi a matsayin dan majalisar a mazaɓarsa ta yankin Ilinois.


A tsawan watani 18 Barack Obama na fafatawa da matar tsofan shugaban ƙasar Amurka, wato Hilary Klinton domin samun tabaraki daga jam´iyar Demokrate don tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasar Amurikar.

Kafin zabe

A shekara ta 2004 ya tsaya takara a Majalisar Dokoki A wani matakin da wasu ke dangatawa da "rabbo rabbabe", babbu zato babu tammaha, Barack Obama ya kai gaci tare da kasa abikiyar hammayar tasa. A duk tsawan wannan lokaci Obama ya bayyana kansa a matsayin gwarzo, duk da cewar da dama na masa zargin rashin ƙurrewa cikin harakokin siyasa, idan aka kwatanta shi da Hilary Klinton, ko kuma da ɗan takara jam´iyar Republicain John Makain, mai shekaru 72 a duniya,wanda kuma ya laƙanci ƙabli da ba´adin siyasa, a ciki da wajen Amurika. Ta fannin rubuce rubuce,Barack Obama, ya rubuta littatafai guda biyu, inda a ɗaya daga cikin su, yayi tarihin rayuwar baƙƙaƙe a Amurika, tare da bayyana yadda a matsayinsa na baƙin ba´amurike ya gudanar da yarintarsa. Barack Obama,na da aure da kuma ´yaya,´yan mata guda biyu.

kafin ya tsaya takara da shi Sanata ne akunjiyar dimukaratic ta Jihara Illinois acikin wannan lokacin a 4 ga 2005 zuwa 16 ga shekara ta 2008 kuma shene dan afirka na farko a majalisar wakilai Amurika kuma shene dan asilim Afirka na farko yatsaya takara shugaban Amurika a kungiyar dimucraic bayan ya tserewa abukiyar takatarsa Hillary Clinton .